Siyasa

Kwankwaso na Shirin Ficewa daga NNPP zuwa ADC

Rahotanni na nuni da cewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa ADC gabanin zaben shekarar 2027.

Majiyoyi sun bayyana cewa Kwankwaso ya dauki wannan mataki ne bayan ya bai wa Buba Galadima umarni ya fara tattaunawa da shugabannin jam’iyyar ADC domin duba yiwuwar komawarsa.

 

Wannan mataki na zuwa ne bayan hukuncin Court of Appeal wanda ya tabbatar da sahihancin shugabancin bangaren NNPP karkashin Agbo Major, sabanin bangaren Ajuji Ahmed da ke goyon bayan Kwankwaso.

A bangare guda kuma, jam’iyyar ADC na kara samun karbuwa a Jihar Kano, musamman sakamakon rawar da tsohon shugaban jam’iyyar APP, Ibrahim Ali Amin ke takawa. Rahotanni sun nuna cewa manyan ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki na yawaita kai ziyara gidansa, lamarin da ke nuna tasirinsa a cikin jam’iyyar a jihar.

 

Sai dai har yanzu ba a cimma matsaya ba dangane da rabon mukamai da tsarin shugabanci a jam’iyyar.

 

ADC na shirin gudanar da zabukan cikin gida a bude ga kowa, tare da bai wa masu neman mukamai dama iri daya—abin da wasu ke ganin ya sha banban da tsarin da Kwankwaso ya saba amfani da shi na cimma matsaya (consensus).

 

Har yanzu dai ba a tabbatar ba ko Kwankwaso zai goyi bayan dan takarar gwamna daga bangarensa ko kuma zai hada kai da sauran masu neman takara irin su Ibrahim Khalil.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button