Ketare

Iran Ta fara kai Hare-haren Ramuwar Gayya kan Israel da United States

Iran ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya bayan hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai mata da safiyar yau, lamarin da ya ƙara dagula yanayin tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Isra’ila, Israel Defense Forces (IDF), ta fitar, ta tabbatar da gano makamai masu linzami da Iran ta harba cikin Isra’ila, tana mai cewa ana ƙoƙarin kakkaɓo su domin rage ɓarna.

Hakazalika, ƙasar Qatar ta tabbatar da cewa Iran ta kai hari kan wasu sansanonin sojin Amurka da ke ƙasarta, amma ta ce an samu nasarar kakkaɓo hare-haren ba tare da an samu mummunar illa ba.

Ita ma Bahrain ta bayyana cewa an kai hari kan sansanonin sojin ruwan Amurka da ke ƙasarta, sai dai ba ta danganta harin da kowace ƙasa kai tsaye ba.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a fitar da cikakken bayani kan asarar rayuka ko ɓarnar da hare-haren suka janyo ba, yayin da ake sa ran ƙarin bayani daga ɓangarorin da abin ya shafa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button