EFCC Ta Gurfanar da Mutanen da Ake Zargi da Karɓar Naira Miliyan 603 Domin Samuwa wav Mukamin GMD a NNPC

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gurfanar da wasu mutane da ake zargi da karɓar kuɗi har Naira miliyan 603,000,000 daga wata mata, bisa zargin yin alƙawarin sama mata mukamin Babbar Daraktar Gudanarwa (GMD) a Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC).
Wacce ake zargin an yaudareta, Oluseye Yomi-Sholoye, ta shaida cewa mutanen sun yi mata alƙawarin cewa za su yi amfani da tasirinsu domin ta samu naɗin mukamin GMD na NNPC, inda ta mika musu kuɗaɗen a matakai daban-daban.
Waɗanda ake tuhuma a shari’ar su ne Gidado Ibrahim da Halimat Adenike Tejusho, wadda rahotanni suka nuna cewa a halin yanzu tana gudun hijira.
An gurfanar da su ne a ranar Litinin a gaban Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya Abuja da ke Maitama, inda EFCC ta gurfanar da su kan ƙarin tuhuma guda shida da suka shafi zamba da karɓar kuɗi ta hanyar yaudara.
A cikin tuhumar, EFCC ta ce ana zargin mutanen da ƙirƙirar wata takarda ta bogi mai taken:
“Presidential Villa State House, Office of the National Security Adviser”,
wadda ake zargin sun yi amfani da ita wajen yaudarar matar.
Sai dai a gaban kotu, Gidado Ibrahim ya musanta dukkan tuhumar da ake masa, yana mai cewa ba shi da hannu a laifukan da aka jingina masa.




