Labarai

Ana zargin wata Amarya da kashe mijinta A jihar jigawa

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Dutse, ranar Asabar.

Ya ce marigayin ya ci abincin rana a gidansa ne kafin daga bisani ya fara jin rashin lafiya mai tsanani.

A cewarsa, an gaggauta kai mutumin zuwa asibiti domin samun kulawar lafiya, sai dai likitoci suka tabbatar da rasuwarsa yayin da ake masa jinya.

SP Adam ya bayyana cewa jami’an bincike daga ofishin ‘yan sandan Jahun sun fara aiki nan take bayan faruwar lamarin, inda suka cafke matar marigayin a matsayin babbar wadda ake zargi.

Ya ce a yayin bincike, wadda ake zargin ta amsa laifin zuba maganin beraye a cikin abincin mijinta, tana mai cewa ta tura ‘yar uwarta ta sayo gubar da aka yi amfani da ita.

Kakakin ‘yan sandan ya ƙara da cewa matar ta bayyana wa masu bincike cewa an tilasta mata auren ne daga iyayenta, lamarin da ta ce ya jawo ta aikata wannan ɗanyen aiki.

Sai dai rundunar ‘yan sandan ta ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar Jigawa ya bayar da umarnin miƙa lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) da ke Dutse, domin gudanar da cikakken bincike.

 

SP Adam ya ce da zarar an kammala binciken, za a gurfanar da wadda ake zargi a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa doka.

 

A halin yanzu, rundunar ‘yan sandan ta yi kira ga al’umma da su kasance masu bin doka da oda, tare da guje wa ɗaukar doka a hannu, musamman wajen magance matsalolin aure da na iyali.

 

Rundunar ta jaddada aniyarta ta tabbatar da adalci da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar Jigawa, tana mai cewa wadda ake zargin na ci gaba da kasancewa a tsare, tana jiran shari’a.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button