Labarai

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta kwashe dukkan fursunoni daga gidan yari na Kurmawa wanda yake tun zamanin mulkin mallaka zuwa wani sabon gidan yari da aka gina a Janguza, inda za ta mayar da tsohon gidan yarin gidan tarihi.

KANO/YARI

Mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai a tawagar gwamna Abba Kabir Yusuf Ibrahim Adam ne ya tabbatar da hakan.

Sabon ginin na Janguza mai dauke da fursunoni 3,000, gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta gina shi.

An gina gidan yarin na Kurmawa ne a shekarar 1910 a karkashin gwamnatin mulkin mallaka. Daga nan ya zama daya daga cikin fitattun alamomin tarihin mulkin mallaka da ke Kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button