Kwamishinan Kimiyya da Fasaha na Kano, Yusuf Kofar Mata, Ya Ajiye Muƙaminsa

Kwamishinan Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire na Jihar Kano, Yusuf Ibrahim Kofar Mata, ya sanar da saukarsa daga muƙaminsa, yana mai cewa matakin ya biyo bayan kaucewa daga tsarin siyasar da aka gina gwamnatin jihar a kansa.
Yusuf Kofar Mata ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, inda ya ce ya yanke shawarar ajiye muƙamin domin bin ƙa’ida da akidar siyasar da aka yi gwagwarmayar kafawa gwamnatin Kano mai ci.
A cikin saƙon nasa, Kofar Mata ya nuna godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki, sannan ya miƙa godiya ta musamman ga jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa damar da suka ba shi na yin hidima.
Haka kuma, ya gode wa al’ummar Jihar Kano bisa goyon baya da haɗin kai da suka ba shi a lokacin da yake gudanar da ayyukansa a Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da Ma’aikatar Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire, tare da jaddada cewa ya aiwatar da muhimman ayyuka domin ci gaban jihar.
Ya kammala saƙon nasa da nuna godiya ga Allah, yana mai cewa, “Alhamdulillah.”
Yusuf Kofar Mata dai shi ne kwamishina na farko da ya ajiye muƙaminsa tun bayan fara rikicin siyasa tsakanin Gwamnan Jihar Kano da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, lamarin da ya ƙara jawo hankalin masu ruwa da tsaki a siyasar jihar.



