Labarai

SHUGABAN SASHEN SIYASA NA HIKIMA RADIO KANO, ALIYU SUFYAN, YA AJIYE AIKI

Jaridar Arewa Updates ta rawaito cewa Aliyu Sufyan ya ajiye aikin ne a ranar Litinin, 2 ga watan Fabrairun 2026.

A cikin wasiƙar murabus ɗinsa, Aliyu Sufyan ya bayyana godiyarsa ga hukumar gudanarwar Hikima Radio da ma’aikatanta bisa kyakkyawar mu’amala, fahimta da mutunta juna da suka yi aiki tare da su a tsawon lokacin da ya yi a tashar.

Bayanai sun nuna cewa ya ɗauki wannan mataki ne domin samun dama da cikakken lokaci na ci gaba da bunƙasa tasharsa ta Siyasarmu TV, wadda ta yi fice wajen gabatar da ingantattun labaran siyasa ba tare da son rai ko ɓangarewa ba.

Aliyu Sufyan dai gogaggen ɗan jarida ne da ya soma koyon aikin jarida a Rediyon Tarayya ta Pyramid FM Kano, kafin daga bisani ya koma Express Radio Kano.

Daga nan kuma ya shiga Aminci Radio tun daga kafuwarta, inda ya shugabanci Sashen Siyasa na tashar tsawon lokaci.

Ana danganta Aliyu Sufyan da taka muhimmiyar rawa wajen gina da ciyar da sashen siyasa na Aminci Radio, tare da ɗaga ƙimar tashar a idon abokan hulɗa da masu sauraro.

Saboda ƙwarewa da gogewarsa a fagen shirye-shiryen siyasa, Aliyu ya samu tayin ayyuka daga tashoshi daban-daban a Kano, sai dai ya zaɓi Hikima Radio, inda shi ma ya riƙe muƙamin Shugaban Sashen Siyasa har zuwa lokacin barin aikinsa.

Ɗan jaridar ya yi fice wajen kyakkyawar mu’amala da ‘yan siyasa, lamarin da ya sa kusan dukkanin manyan ‘yan siyasa da ke Kano ke neman ƙulla alaƙa da shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button