Armed Conflict Location & Event Data Project (ACLED) Ta Yi Gargaɗin Ƙaruwar Rikice-rikice a Kan Iyakokin Najeriya

Wani sabon bincike da ƙungiyar ACLED ta fitar ya nuna cewa yankin kan iyakar Najeriya da ƙasashen Benin da Jamahuriyar Nijar na neman zama sabuwar cibiyar rikice-rikice a shekarar 2025.
A cikin rahoton da ta wallafa ranar Alhamis, ACLED ta bayyana cewa an samu gagarumar ƙaruwar hare-hare a yankin cikin shekarar da ta gabata, lamarin da ke nuna ƙara tsananta matsalar tsaro.
Rahoton ya kuma nuna cewa a cikin makon nan kaɗai an kai hare-hare sau biyu a Jihar Kebbi, inda aka ruwaito cewa Lakurawa sun kashe gomman mutane.
A cewar ACLED, rikice-rikicen na da alaƙa da ƙungiyoyin Jama’at Nasr al-Islam wal Muslimin (JNIM) mai biyayya ga Al-Qaeda da kuma Islamic State in the Greater Sahara (EIS) mai alaƙa da ISIS. Ƙungiyoyin biyu ne ke da alhakin kashi 86 cikin 100 na ƙaruwar hare-haren idan aka kwatanta da shekarar 2024.
Bugu da ƙari, rahoton ya nuna cewa an samu ƙaruwar kashe-kashe da kashi 262 cikin 100 a yankin, abin da ke ƙara tayar da hankalin hukumomi da al’umma kan buƙatar ƙarin matakan tsaro.



