Labarai

NDLEA Ta Ƙaddamar da “Operation Ramadan Mubarak” a Kano

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) reshen Jihar Kano ta ƙaddamar da wani aiki na musamman mai taken “Operation Ramadan Mubarak” a wasu sassan birnin Kano.

 

Aikin, wanda aka fara a ranar Alhamis, ya shafi gudanar da sintiri na musamman a unguwannin Kofar Mata, Ɗan Zaki, Fagge da Kofar Wambai.

 

Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar a Kano, Sadiq Muhammad Mai Gatari, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Sai dai zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumar ba ta fitar da cikakken bayani kan sakamakon aikin ba.

 

An dai bayyana cewa aikin na daga cikin matakan da hukumar ke ɗauka domin daƙile safarar miyagun ƙwayoyi da kuma tabbatar da tsaro a lokacin watan Ramadan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button