Hukumar karota zata kawo karshen matsalar da ake samu tsakanin jami’anta da jami’an soji

Hukumar Kula da Harkokin Sufuri da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ta sake jaddada kudirinta na ci gaba da aiki kafada da kafada da rundunonin sojoji da ke aiki a jihar domin ci gaban kasa baki daya.
Wannan tabbaci ya fito ne daga bakin Shugaban KAROTA, Hon. Faisal Mahmud Kabir, a lokacin da Kwamandan Makarantar Horar da Matukan Jiragen Sama ta 403 Flying Training School da ke Kano, Group Captain Uchenna Ihediwa, ya kai masa ziyarar girmamawa a ofishinsa.
Hon. Faisal Mahmud ya bayyana cewa duk da an samu wasu ‘yan matsaloli a baya tsakanin jami’an KAROTA da wasu jami’an soja, hukumar na kokarin warware duk wata rashin fahimta ta hanyar zaman lafiya da fahimtar juna.
Ya kuma tabbatar da cewa KAROTA za ta ci gaba da inganta kyakkyawar alaka da dukkan rundunonin sojoji da ke jihar, tare da godiya ga ziyarar da Kwamandan Rundunar Sojin Sama ya kai masa, inda ya ce dangantaka za ta kara karfi da inganci a nan gaba.
A nasa bangaren, Group Captain Uchenna Ihediwa ya bayyana cewa manufar ziyarar tasa ita ce kara dankon zumunci tsakanin makarantar horas da matukan jiragen sama ta rundunar sojin sama da hukumar KAROTA, domin su hada kai wajen tabbatar da doka da oda a tsakanin al’umma.
Ya jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin dukkan jami’an da ke sanya kayan aiki na hukuma domin su sauke nauyin da kundin aikinsu ya dora musu yadda ya kamata.
Kwamandan ya kara da cewa kula da zirga-zirgar ababen hawa na bukatar tsantsar tsaro, taka-tsantsan, hadin kai da kwarewa, inda ya yaba wa jami’an KAROTA bisa jajircewarsu da sadaukarwarsu wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
Daga karshe, ya gode wa Shugaban KAROTA bisa tarbar da aka yi musu, tare da yin alkawarin samar da karin hanyoyin da za su tabbatar da dorewar kyakkyawar alaka tsakanin bangarorin biyu.




