Ketare
Dimokraɗiyya ba ta dace da Burkina Faso ba – Traore

Shugaban mulkin sojin Burkina Faso ya shaida wa al’ummarsa su daina sa rai da dimokuraɗiyya.
A wata hira da aka watsa a gidan talabijin na ƙasa, Kyaftin Ibrahim Traore ya ce ba shi da wani shiri na gudanar da zaɓe, duk da cewa ya yi alƙawarin mayar da mulki ga farar hula lokacin da ya karɓi iko shekaru huɗu da suka gabata.
Sai dai a ranar Alhamis, ya bayyana a fili cewa dimokuraɗiyya ba ta dace da al’ummar Burkina Faso ba.
Gwamnatinsa ta soja ta gaza shawo kan rikicin tashe-tashen hankulan masu iƙirarin jihadi da suka addabi ƙasar.
Haka kuma, ƙungiyoyin kare hakkin ɗanadam na ci gaba da suka kan kamun ludayin gwamnatinsa ta fuskar ƴancin ɗan’adam.



