Mutum 1,296 aka kashe a Najeriya a watan Mayu – Rahoto

Wasu sabbin alƙalumma kan matsalar tsaro a Najeriya sun nuna cewa mutum 1,296 aka kashe a watan Mayu a sassan ƙasar.
Rahoton na kamfanin Beacon Consulting da ke nazarin tsaro a shiyyar Afirka ta yamma da yankin Sahel ya ce an samu ƙaruwar yawan waɗanda suka mutu a watan Mayu idan aka kwatanta da Afrilu inda aka kashe mutum 1,092.
Rahoton ya kuma ce mutum 1,086 aka yi garkuwa da su a sassan Najeriya a watan Mayu inda aka samu ragi idan aka kwatanta da watan Afrilu da aka yi garkuwa da mutum 1,178.
Rahoton Beacon Security and Intelligence Limited ya nuna cewa an samu ragi na kashi kusan shida cikin dari na matsalolin tsaro a Najeriya cikin watan Mayun da ya gabata, idan aka kwatanta da yadda lamarin ya kasance a watan watan Afrilu da ya gabace shi.
Sai dai an sami karuwar kashi goma sha tara cikin dari na mace-macen da suka auku a sakamakon matsalar ta tsaro a cikin watan na Mayu.
Rahoton ya nuna cewa ragin da aka samu bai rasa nasaba da ƙoƙarin da jami’n tsaron ƙasar ke yi na yaƙi da matsalolin tsaro a sassan ƙasar.
Jihar Zamfara ce ta fi yawan mutanen da aka fi kashe wa, domin an kashe mutane a watan Mayu da suka kai (332) a jahar Zamfara, sai jihohin Borno da Katsina da Kebbi da kuma Neja, a cewar Rahoton na Beacon Consulting.
Kamfanin ya ce ya tattara alƙalumman ne ta hanyar rahotannin hare-hare da kashe-kashe da ake bayarwa a kafafen yaɗa labarai da kuma rahotannin jami’an kamfanin a sassan Najeriya.
Rahoton ya ayyana cewa Najeriya na ci gaba da fuskantar kalubale ta fannin tsaro a sassan kasar da dama, kasancewar ana fama da matsalar harin ƴan bindiga da wasu kungiyoyi, ciki hár da Boko Haram da ta IPOB, masu fafutukar ballewa da nufin kafa kasar Biafra.
Muhukunta a Najeriya a matakai daban-daban dai kan yi ikirarin daukar matakai don inganta tsaro, amma za a iya cewa matsalar na nan ba ta kau ba.
A hirarsa da BBC, shugaban kamfanin tsaron na Beacon Malam Kabiru Adamu ya ce akwai bukatar gwamnatoci a matakai daban-daban su fitar da tsarin da zai gaggauta rage talauci a tsakanin al’umma, sannan a kyautata tsarin yaƙi da ta`addanci ta hanyar cusa al`umma a ciki, wato ta yadda za su dinga samar da bayanai ga jami`an tsaro da bangarorin da yaƙi da ta`addancin ya shafa.
BBC Hausa (https://www.bbc.com/hausa/articles/cwyn4p3w1nlo?at_campaign=ws_whatsapp)



