Ƙungiyoyin Tijjaniyya da Ƙadiriyya Sun Garzaya Kotu Kan Zargin ɓatanci a Kano

Ƙungiyoyin Tijjaniyya da Ƙadiriyya a jihar Kano sun garzaya gaban kotu, inda suka roƙi kotun ta tilastawa gwamnatin jihar Kano gurfanar da Lawan Abubakar Triumph a gaban shari’a kan zarge-zargen ɓatanci ga Annabi Muhammadu (SAW).
Lauyoyin ƙungiyoyin, ƙarƙashin jagorancin Barrister Hashim Hussaini Fagge, sun bayyana wa kotu cewa sun shigar da ƙarar ne domin neman umarnin kotu da zai wajabta wa gwamnan Kano ɗaukar matakin shari’a tare da gurfanar da wanda ake zargi bisa doka.
A cewarsu, zargin da ake yi na da muhimmanci matuƙa ga zaman lafiya da mutunta addini, don haka suka nemi kotu ta shiga tsakani domin a bi tsarin doka yadda ya kamata.
A nasa ɓangaren, lauyan gwamnatin jihar Kano, Barrister Lamido Abba Soron Ɗinki, ya roƙi kotun da ta ɗage sauraron shari’ar, yana mai cewa gwamnatin ba ta kammala shirya amsar da za ta bayar kan buƙatar da aka gabatar ba a wannan lokaci.
Kotun dai ta saurari ɓangarorin biyu, sannan ta ɗage shari’ar zuwa wata rana domin bai wa gwamnatin jihar damar shiryawa da gabatar da cikakkiyar amsa.




