Labarai

Gwamnatin Kano Ta Karyata Zargin Hana ‘Yan Adawa ’Yancin fadar albarkacin baki

Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da zargin da wani ɗan siyasa daga Jihar Yobe, Buba Galadima, ya yi cewa ana hana wasu ’yan adawa gudanar da haƙƙoƙinsu na siyasa a jihar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai, inda ya bayyana zarge-zargen a matsayin ƙarya, marasa tushe, kuma marasa hujja ingantacciya.

Waiya ya jaddada cewa gwamnatin Kano na nan daram kan bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya da kuma kare haƙƙoƙin kundin tsarin mulki na kowane ɗan ƙasa ba tare da la’akari da jam’iyyarsa ba.

 

Ya ƙara da cewa jihar na mutunta ’yancin faɗar albarkacin baki, ’yancin haɗuwa da kuma cikakken shiga harkokin siyasa.

Ya bayyana cewa gwamnatin ba ta tsoma baki cikin halattattun ayyukan kowace jam’iyya ko ɗan siyasa ba, tare da ƙalubalantar masu wannan zargi da su gabatar da hujja tabbatacciya.

Kwamishinan ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnati za ta ci gaba da ƙarfafa siyasa mai cike da zaman lafiya tare da tabbatar da daidaito ga duk masu ruwa da tsaki a harkar siyasa.

Sai dai Waiya ya zargi Galadima da rasa fahimtar halin siyasa a jiharsa da kuma a matakin ƙasa, yana mai cewa yana da ’yancin bayyana ra’ayinsa amma ya kamata ya yi hakan cikin gaskiya da ɗaukar alhaki.

Haka kuma, ya ce Galadima na jin zafi tun bayan cire shi daga muƙamin shugaban majalisar gudanarwa ta Kwalejin Fasaha ta Kano (Polytechnic), lamarin da ya ce ya haifar masa da fushi.

A cewar Waiya, tun lokacin da aka naɗa Galadima a matsayin shugaban majalisar kwalejin, bai bayar da wata gudummawar jagoranci ba, kuma bai kira wani taro da zai taimaka wajen bunƙasa makarantar ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button