Siyasa

Kwankwasiyya Ta Musanta Rahoton Rashin Lafiyar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Ƙungiyar siyasa ta Kwankwasiyya ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke iƙirarin cewa an fita da jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ƙasar waje domin neman lafiya.

Mai magana da yawun ƙungiyar Kwankwasiyya a Najeriya, Captain Mansur Kurugu, ya shaida wa BBC cewa balaguron da Kwankwaso ya yi zuwa ƙasar waje ba shi da alaƙa da rashin lafiya, sai dai wata buƙata ta kansa.

A cewarsa, “Abin da ke ƙara tabbatar da hakan shi ne, ranar Laraba kafin balaguronsa, Kwankwaso ya shiga Jihar Kano inda ya gana da mutane daban-daban.

Haka kuma a safiyar Alhamis, dubban mutane daga ƙaramar hukumar Dawakin Kudu sun kawo masa ziyara, inda aka tattauna, kafin ya wuce kasuwar Singer domin jajantawa ƴan kasuwar da suka rasa dukiyoyinsu.”

Mansur Kurugu ya jaddada cewa mutumin da ke fama da rashin lafiya ba zai iya gudanar da irin waɗannan ayyuka ba, yana mai cewa wasu da ba su ji daɗin tarbar da aka yi wa Kwankwaso a kasuwar Singer ba ne suka ƙirƙiro labarin.

“Babu wata magana ta rashin lafiya ko wata damuwa. Waɗanda ke jin tsoro ne kawai ke ƙoƙarin yaɗa irin waɗannan labarai domin rage karɓuwar da Kwankwaso ke ƙara samu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ana sa ran jagoran Kwankwasiyyar zai dawo Najeriya nan ba da daɗewa ba bayan ya kammala abin da ya kai shi ƙasar waje.

Rahotannin balaguron Kwankwaso zuwa ƙasashen waje dai sun bazu a kafafen sada zumunta, lamarin da ya haifar da cece-kuce a tsakanin jama’a

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button