Labarai

Al’ummar Birni Sun Kira Gwamnan Kano Ya Ci Gaba da Gina Dakin Adana Kayan Tarihi na Northwest University

Al’ummar Karamar Hukumar Birni a Jihar Kano sun yi kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya sake waiwaye tare da ci gaba da aikin gina dakin adana kayan tarihi da kayan koyo da koyarwa na Jami’ar Northwest University Kano.

A cewar al’ummar yankin, an fara aikin ginin ne a lokacin mulkin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, inda aka gina katafaren dakin ajiya na kayan karatu da muhimman abubuwan tarihi a kan titin Gidan Sarki, wurin da a baya yake gidan marigayi Dan Masanin Kano.

 

Sai dai bayan hawan Gwamna Abba Kabir Yusuf, aikin ginin ya tsaya cik, wanda al’ummar yankunan Durumin Zungurawa, Kankarofi, Yakasai, Durumin Iya, Kurmawa, Sharada da Yar Magaji suka ce hakan ne ya sa suka nemi gwamnatin jihar ta sake duba lamarin.

Sun bayyana cewa kammala wannan katafaren dakin adana kayan tarihi da kayan koyarwa zai taimaka matuƙa wajen bunƙasa ilimi, adana tarihin Kano, da kuma kawo ci gaba ga jihar Kano baki ɗaya, musamman ga ɗalibai da masu bincike.

Duk da kiran da suke yi, al’ummomin yankin sun yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan ayyukan raya ƙasa da yake aiwatarwa a faɗin jihar, tare da bayyana fatan cewa zai ɗauki matakin gaggawa domin kammala aikin da ke da matuƙar muhimmanci ga Kano da ƙasa baki ɗaya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button