Sanata Barau Jibrin Ya Kafa Kwamitin Mutane 51 a Kowace Karamar Hukuma Don Shirya Zaben 2027

Sanata Barau I. Jibrin ya ɗauki sabbin matakai na ƙarfafa goyon bayan jam’iyyar APC a Jihar Kano, inda ya kafa kwamitin mutum 51 a kowace ƙaramar hukuma domin gudanar da ayyukan yaƙin neman zaɓensa.
Sai dai daga bisani, an umarci waɗannan kwamitoci da su karkata akalar ayyukansu wajen yi wa Shugaban Ƙasa da kuma Gwamnan Kano yaƙin neman zaɓe, a wani yunkuri na haɗa ƙarfi wuri guda.
A ƙaramar hukumar Dala, an raba tallafin kuɗin miyar Sallah naira 20,000 ga kowane memba na kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Hon. Sidi Kabuwaya, yayin da Comrade Alhassan Uba Idris ke taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar shirin.
Rahotanni sun nuna cewa dukkanin mambobin kwamitin sun amfana da wannan tallafi domin sauƙaƙa musu gudanar da bukukuwan Sallah.
A wani ɓangare na daban kuma, ƙungiyar Comrade Alhassan Uba Idris Solidarity Forum a Dala ta raba kuɗaɗen tallafi da suka kai kusan naira miliyan huɗu ga mambobinta daga mazabu 12 na ƙaramar hukumar, domin tallafa musu a yayin bukukuwan Sallah.
Shugaban ƙungiyar, Hon. Aminu Baba Ali (Travelled), ya bayyana jin daɗinsa kan yadda jagoran ƙungiyar ke tallafawa ‘ya’yan jam’iyyar APC a yankin, yana mai cewa hakan na ƙara haɗin kai da ƙarfafa jam’iyyar a matakin ƙasa.




