Atiku Ya Soki Yunkurin Kama El-Rufai

Jagoran adawa na jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yunƙurin kama Malam Nasiru El-Rufai tamkar yunƙurin yin garkuwa da shi ne.
Atiku ya yi wannan furuci ne yayin wata ziyara da ya kai gidan tsohon gwamnan a jiya, inda ya ce abin da ya faru a filin sauka da tashin jiragen sama na Abuja cin fuska ne ga ƙasar nan.
Ya ƙara da cewa El-Rufai mutum ne mai daraja da ya cancanci a mutunta shi, kasancewarsa tsohon gwamna kuma tsohon minista.
Jagoran adawar ya jaddada cewa ba za su zuba ido ana cuzguna wa ’yan adawa ba, yana mai zargin cewa suna sane da ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na lalata tsarin jam’iyyar ADC.
A cewarsa, ba za su lamunta hakan ba.
Rahotanni sun nuna cewa takaddamar ta taso ne a filin jirgin saman Abuja bayan dawowar El-Rufai daga ƙasar Masar, inda jami’an DSS suka buƙaci ya amsa gayyatar su.



