Labarai

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tsayar da Hukuncin Kisa Kan Masu Fashi Biyar

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Ilorin, jihar Kwara, ta tabbatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya da Babbar Kotun Jihar Kwara ta yanke wa mutane biyar da aka samu da laifin fashi da makami a wani mummunan fashin banki da ya auku a garin Offa a shekarar 2018.

 

Daraktan Sashen Shigar da Ƙara na Jihar Kwara, Mohammed Akande, ya bayyana cewa dukkan alƙalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙara sun amince da hukuncin da kotun ƙasa ta yanke, bayan nazari kan dukkan hujjojin da bangarorin biyu suka gabatar.

 

A cewar wani jami’in kotun, alƙalan sun yi watsi da dukkan ƙorafe-ƙorafen da waɗanda aka yankewa hukuncin suka shigar, tare da ba da umarnin a mayar da su gidan yari cikin gaggawa.

 

Sai dai, jami’in ya bayyana cewa doka ta ba waɗanda aka yanke wa hukuncin damar ƙalubalantar hukuncin a Kotun Ƙoli, amma ya jaddada cewa hujjojin da suka gabatar a Kotun Ɗaukaka Ƙara ba su gamsar ba, kuma akwai ƙarancin yiwuwar samun sauyi idan aka maimaita irin waɗannan hujjoji a matakin ƙarshe na shari’a.

 

Hukuncin ya samo asali ne daga fashin banki da aka kai a watan Afrilun 2018 a ƙaramar hukumar Offa, inda aka kai hari kan bankunan kasuwanci guda biyar a lokaci guda.

 

Aƙalla mutane 32 ne suka rasa rayukansu a yayin harin, ciki har da ‘yan sanda tara, daga cikinsu mata biyu, lamarin da ya sa aka bayyana fashin a matsayin ɗaya daga cikin mafi muni a tarihin Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button