An Shirya Saukar Alƙur’ani a Kano Domin Neman yardar Allah kan Gawuna Ya Koma Kwankwasiyya

An shirya gudanar da saukar Alƙur’ani mai girma a jihar Kano domin yin addu’ar neman tsohon mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Yusuf Gawuna, ya amsa kiran komawa tafiyar Kwankwasiyya.
Rahotanni sun nuna cewa, wannan shiri na cikin wata sanarwa da Ahmad Sabo Gama ya fitar a madadin shugabannin wata ƙungiya da ke goyon bayan Gawuna, inda ya bukaci magoya baya da ’yan uwa su taru domin wannan muhimmin aiki na addini.
A cewar sanarwar, za a gudanar da taron ne a ranar Juma’a, 27 ga Maris 2026, da misalin ƙarfe 3:00 na rana, a masallacin da ke ƙofar gidan Gawuna da ke unguwar Miller Road a Kano.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa an gayyaci daukacin masoya, abokai da ’yan uwa domin halartar wannan taro, inda za a yi addu’o’i na musamman domin neman alkhairi da dacewa kan wannan kudiri.
Masu shirya taron sun jaddada muhimmancin hadin kai da addu’a wajen cimma muradun al’umma, tare da fatan wannan yunkuri zai haifar da sakamako mai kyau.
Arewa Updates




