Beatrice Ekweremadu Ta Dawo Najeriya Bayan Sakinta Daga Gidan Yarin Birtaniya

Beatrice Ekweremadu, matar tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ike Ekweremadu, ta dawo Najeriya a ranar Talata, 21 ga Janairun 2026, bayan an sake ta daga gidan gyaran hali a ƙasar Birtaniya.
Wannan ne karo na farko da Mrs. Ekweremadu ta taka ƙafa ‘a Najeriya tun bayan fara shari’ar da ta shafi dangin Ekweremadu a tsakiyar shekarar 2022.
An tarbe ta a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja daga ‘yan uwa, abokan arziki da magoya baya, yayin da al’ummar garin haihuwarta na Mpu da ke Jihar Enugu suka gudanar da murnar dawowarta gida.
Mrs. Ekweremadu ta samu hukuncin ɗaurin shekaru huɗu da watanni shida a watan Mayun 2023 daga Kotun Old Bailey da ke Landan, bisa laifin shirin kai wani matashi ɗan shekaru 21 daga Lagos zuwa Birtaniya domin cire masa koda ba bisa ƙa’ida ba, domin ceto rayuwar ‘yarsu, Sonia, wadda ke fama da matsananciyar matsalar koda.
An gudanar da shari’ar ne ƙarƙashin Dokar Cin Zarafin Mutane ta Birtaniya ta shekarar 2015, wanda shi ne karo na farko da aka yi amfani da dokar a shari’ar da ta shafi satar gabobin jiki.
Rahotanni sun nuna cewa kyakkyawan ɗabi’ar Mrs. Ekweremadu a gidan yari da kuma shirin gwamnatin Birtaniya na rage cunkoson fursunoni ne suka taimaka wajen sake ta kafin cikar wa’adin hukuncinta.
Sai dai mijinta, Sanata Ike Ekweremadu, na ci gaba da zaman ɗaurin shekaru tara da watanni takwas a wani gidan gyaran hali a Birtaniya, bayan da kotu ta tabbatar da shi a matsayin babban mai tsara shirin.
Ƙoƙarin gwamnatin Najeriya na dawo da shi gida ta hanyar Yarjejeniyar Canja Wurin Fursunoni (PTA) ya ci tura a watan Nuwamban 2025, sakamakon damuwar yadda za a aiwatar da hukuncinsa a Najeriya.
A halin yanzu, Dr. Obinna Obeta, wanda shima aka samu da laifi a shari’ar, na ci gaba da zaman ɗaurin shekaru 10 a Birtaniya.
Ita kuwa Sonia Ekweremadu, wadda kotu ta wanke daga dukkan tuhuma, na ci gaba da karɓar magani a Birtaniya bisa matsalar kodarta.



