Labarai
Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa ta ce ta yi nasarar gano ababen hawa 35 da aka sace a faɗin ƙasar cikin wata shidan farko na shekarar 2025.

Mai magana da yawun hukumar ta Federal Road Safety Corps (FRSC), Olusegun Ogungbemide, ne ya bayana hakan a cikin wata sanarwa ranar Juma’a
Yace sun yi nasarar ne sakamakon tsarinsu na rajistar ababen hawa ta intanet mai suna National Vehicle Identification Scheme (NVIS).
Ya ce an sace motocin ne ta hanyoyi daban-daban, ciki har da fashi, da garkuwa da mutane, da zamba.



