Labarai

Zargin sayan kuri’a EFCC ta kama mutane 20 a Abuja

Hukumar EFCC ta sanar da kama mutum 20 da ake zargi da aikata laifukan zaɓe yayin zaɓen ƙananan hukumomin Babban Birnin Tarayya Abuja, da aka gudanar a ranar 21 ga Fabrairu, 2026.

A cewar hukumar, an kama mutanen ne a wurare daban-daban bisa zargin sayen ƙuri’u, sayar da ƙuri’u da kuma hana jami’an zaɓe gudanar da aikinsu.

 

An kuma ce an gano kuɗaɗe har Naira miliyan 17,218,700 a hannun waɗanda ake zargin.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale, ya fitar, an bayyana cewa an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da Naira miliyan 13,500,000 a cikin wata mota da aka ajiye kusa da rumfar zaɓe a yankin Kwali.

Sanarwar ta ƙara da cewa an kama mutane biyu a Abaji, tara a Gwagwalada, huɗu a Kuje, sannan huɗu a Kwali.

 

Hukumar ta ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu bayan kammala bincike.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button