Rasuwar Jaruma Hajiya Halimatus Sadiya ‘Sabuwa’ Ta Girgiza Masoya Shirin Dadin Kowa

Allah ya yi wa fitacciyar jarumar Kannywood, Hajiya Halimatus Sadiya, wacce aka fi sani da Sabuwa a cikin shirin Dadin Kowa na tashar Arewa24, rasuwa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yarta Amina, wadda aka fi sani da Raliya ƴar bijilanti a cikin shirin Dadin Kowa, ita ce ta tabbatar da rasuwar ga manema labarai.
Marigayiyar ta kasance gogaggiyar jaruma a masana’antar Kannywood, inda ta kwashe sama da shekaru 20 tana taka rawa a fina-finai daban-daban kafin ta shiga cikin shirin Dadin Kowa, wanda ya ƙara ɗaga darajarta a idon masu kallo.
Ta shahara matuƙa a matsayin Sabuwa, matar Malam Ayuba mai gadi kuma mahaifiyar Dan Asabe, inda aka santa da haƙuri, hikima da kuma kishin tarbiyyar iyali—halaye da suka sa ta zama abar so ga dubban masu kallon shirin.
A baya, marigayiyar ta taɓa bayyana ƙalubalen da take fuskanta na ƙangin rayuwa, lamarin da ya janyo muhawara a masana’antar.




