Labarai

Gwamnan Sokoto Ya Shirya Gabatar da Dokar Haramta Almubazzaranci yayin bikin Aure

Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta gabatar da dokokin haramta abin da ya kira almubazzaranci a lokacin aure a faɗin jihar.

 

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a yayin ƙaddamar da masallaci da makamarantar zawiyya ta Sheikh Aliyu Bunza da aka sabunta.

Ahmad Aliyu ya ce:

“Matakin ya zama wajibi saboda yadda ake samun ƙaruwar wahalhalun da ake ɗorawa mutanen da ke shirin yin aure ta hanyar tsara abubuwan da ba za su zama wajibi ba, lamarin da ke sa matasa maza da mata su sha wahala kafin aure.”

Gwamnan ya jaddada cewa tsadar abubuwan da ake buƙata kafin aure na haifar da ƙaruwar yawan marasa aure da kuma rashin tarbiyya tsakanin matasa a jihar.

Wannan mataki na gwamna na zuwa ne bayan bullowar wani bidiyo a shafukan sada zumunta da ya nuna wata yarinya a jihar Sokoto tana samun kayan lefe masu tsada, ciki har da motar hawa, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin al’umma.

Gwamnan Ahmad Aliyu ya ce dokar da za a gabatar za ta kasance wata hanya ta rage almubazzaranci a aure da tabbatar da cewa matasa za su iya yin aure ba tare da tsadar abubuwa da ake ƙirƙira ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button