Ketare
Rundunar tsaron Amurka ta buƙaci ƙarin aƙalla fam miliyan 150 domin yaƙin Iran

Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya ce Pentagon na buƙatar ƙarin kuɗaɗe daga lalitar gwamnatin ƙasar domin ci gaba da yaƙi a Iran.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambaya kan rahotan da ke nuna sun buƙaci kuɗaɗe a yaƙin, wanda Amurka da Isra’ila ke yi a Iran.
Hegseth sai ya ce kuɗin da ake magana suna neman ƙari wato dala biliyan 200bn kimanin fam miliyan 150 ne, amma ya ƙara da cewa, “kuɗin ma zai iya haura haka.”
“Ana buƙatar kuɗi sosai domin kashe mugayen mutane,” in ji Hegseth, sannan ya nanata cewa, “suna samun duk goyon bayan da suke buƙata.”




