Yan Sandan Kano Sun Miƙa Motar Toyota ga Mai Ita

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta miƙa wata motar Toyota Sienna mai launin ruwan dorawa (maroon) da lambar rajista RBC-801HM ga halalcin mai ita, Malam Ali Alti, bayan nasarar sake gano motar da aka sace.
A cewar sanarwar rundunar, motar wadda kimarta ta kai naira miliyan ashirin (₦20,000,000), wani mai gadi ne ya sace ta daga unguwar Maiduguri GRA da ke Jihar Borno a ranar 5 ga Janairun 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa bisa umarnin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, kan ƙarfafa sintirin tsaro na zamani da ke amfani da bayanan sirri, jami’an ‘yan sanda daga sashen Hotoro a Kano sun yi nasarar gano motar a unguwar Hotoro Arewa a ranar 7 ga Janairun 2026.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin a miƙa motar ga Malam Ali Alti bayan tabbatar da sahihancin takardun mallakarsa.
Sanarwar ta ƙara da cewa mutane huɗu na hannun hukuma kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a kansu dangane da satar motar da aka yi a Maiduguri.
Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu taka-tsan-tsan wajen ɗaukar ma’aikatan gida ko masu gadin tsaro, domin kauce wa aikata laifuka.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta yaba da ƙoƙarin jami’anta tare da gode wa al’umma bisa haɗin kai da goyon bayan da suke ba ta wajen yaƙi da aikata laifuka a jihar.



