Siyasa

A kalla Kwamishinoni 5 da jami’an gwamnati 10 ne suka ajiye muƙamansu

Daga cikin Kwamishinonin da suka yi murabus akwai:

Kwamishinan Matasa da Wasanni, Mustapha Rabiu Kwankwaso

Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dr. Yusuf Kofarmata

Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Nasiru Sule Garo

Kwamishinan Jin Kai, Adamu Kibiya

Kwamishinan Tsaro, AVM Ibrahim Umar

Haka kuma, wasu manyan jami’an gwamnati sun ajiye muƙamansu, ciki har da:

Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u

Shugaban Hukumar Gidan Zoo, Hon. Sadiq Kura Muhammad

Shugaban Hukumar KARMA, Alhaji Hassan Danbappa

SSA GSM Market, Hon. Sani Shehu Makarya (Igwe China)

Sauran sun haɗa da:

Walidin Kwankwasiyya mai taimaka wa gwamna kan harkokin masarautu

Hajiya Ain Jafaru Fagge mai ba gwamna shawara kan yaɗa kyakkyawan saƙo

Mujtaba Muhammad Auwal, jami’in alhazai na Karamar Hukumar Gwale

Hon. Nafiu Umar Dankura, SSA Protocol Abuja

Aminu Sa’idu Meenan Kwankwasiyya da Shafa’atu Ahmed LondonBe, masu riƙe da muƙamin babban masu ɗaukar rahoto ga gwamna a ma’aikatu daban-daban

A cikin bayanan murabus ɗin, jami’an sun bayyana cewa sauye-sauyen siyasa da rikicin da ya kunno kai a jihar ne suka sa suka ɗauki wannan mataki, tare da tabbatar da ci gaba da goyon bayan tafiyar Kwankwasiyya da jagoranta Engr.Rabi’u Musa Kwankwaso.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button