Spain Ta Hana Amurka Amfani da Sansanoninta Domin Kai Hari Kan Iran

Gwamnatin Spain ta ƙi bai wa Amurika izinin amfani da sansanoninta na soji da ke Rota da Morón a kudancin ƙasar domin kai hari kan Iran.
Rahotanni sun ce wasu jiragen sojin Amurka sun bar sansanonin bayan matakin da Madrid ta ɗauka na hana amfani da wuraren wajen duk wani farmaki.
Ministan harkokin wajen Spain, José Manuel Albares, ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta amince a yi amfani da yankinta ba ga “duk wani abu da bai yi daidai da ƙundin tsarin United Nations ba.”
Matakin na Spain ya sa ta saɓa wa ra’ayin wasu ƙawayenta na Turai.
Sai dai babban sakataren NATO, Mark Rutte, ya shaida wa BBC cewa Turai na goyon bayan harin Amurka a Iran.
Duk da haka, firaministan Spain, Pedro Sánchez, ya soki matakin da Amurka da Isra’ila suka ɗauka kan Iran, yana mai jaddada matsayar ƙasarsa na bin dokokin ƙasa da ƙasa.



