Uncategorized

Rahoto: Drop Site News Ta Bankado Zargin Haɗin Gwiwar Jeffrey Epstein da Ehud Barak Kan Batun Tsaron Najeriya

Wani bincike da kafar yaɗa labarai ta Drop Site News (DSN) ta gudanar ya yi zargin cewa hamshaƙin attajirin Amurka, Jeffrey Epstein, da tsohon Firayim Ministan Isra’ila, Ehud Barak, sun yi haɗin gwiwa na tsawon sama da shekara goma domin tsara wasu harkoki da suka shafi ƙalubalen tsaron Najeriya.

Rahoton ya bayyana cewa ana zargin mutanen biyu sun yi aiki tare na dogon lokaci, inda ake cewa sun yi anfani da matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya wajen samar wa kansu riba da wasu muhimman muradun sirri a matakin ƙasa da ƙasa.

 

Binciken ya ƙara da cewa ana alakanta haɗin gwiwar tasu da harkokin kuɗi da tsare-tsare da suka shafi yankunan da ke fama da matsalolin tsaro a Najeriya.

Wannan zargi ya janyo tambayoyi da dama kan yadda ake tafiyar da wasu harkoki da suka danganci tsaro da zuba jari a ƙasar.

Sai dai rahoton ya jaddada cewa ana ci gaba da bincike kan lamarin, yayin da ake sa ran ƙarin bayanai za su fito domin fayyace gaskiyar abin da ake zargi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button