Labarai
Allah yayi wa tsohon Alkalin alkalai na kasarnan mai sharia Muhammed Lawal Uwais rasuwa yana da shekaru 89 a duniya.

Muhammad Lawal Uwais wanda ya rike shugabancin Alkalin alkalai na kasa na tsawon shekaru 11 daga shekarar 1995 zuwa 2006 ya rasu ne a yau Jumaa kamar yadda iyalan sa suka shaidawa manema labarai.
Za’a gudanar da jana’izar sa kowanni lokaci daga yanzu.
Marigayin shi ya taba shugabntar wata hukuma da ta taba wallafa wani rahoto akan sauya tsarin zabe da aka yi ta cece kuce a kai a shekarar 2008.




