Amurka ta bai wa Najeriya kayan aikin soji a Abuja

Rundunar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X a yau Talata.
A cewar sanarwar, tallafin zai taimaka wa kasarnan wajen aiwatar da ayyukanta na tsaro, tare da ƙara ƙarfafa alaƙar tsaro da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Sanarwar ta zo ne tare da hoton wani jirgin dakon kaya da ƙofarsa a buɗe, inda aka hango kayayyaki jibge a kusa da jirgin.
Sai dai rundunar ba ta bayyana takamaiman irin kayan da aka kawo ba.
Najeriya dai na fuskantar ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da matsalar ƙungiyar Boko Haram a arewa maso gabas, hare-haren ƴan bindiga a arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, da kuma ayyukan ƴan aware a kudu maso gabashin ƙasar.
A wani lamari da ke nuna zurfin haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu, a ranar 25 ga Disamban 2025, Amurka ta bayyana cewa ta kai hari kan ƴan bindiga masu alaƙa da ƙungiyar IS a jihar Sokoto.




