Shugaban kasar Nigeriya ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa ƙasar na kan hanya madaidaiciya zuwa ga murmurewa da ci gaban tattalin arziki.
A cikin saƙonsa na bikin Sallah na shekarar 2025, Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa ƙasar na kan hanya madaidaiciya zuwa ga murmurewa da ci gaban tattalin arziki.
Ya amince da wanzuwar wahalhalun da ‘yan ƙasa ke fuskanta sakamakon wasu gyare-gyare da gwamnatinsa ta aiwatar, amma ya bayyana gamsuwa cewa waɗannan matakai sun fara haifar da sakamako mai kyau.
Tinubu ya bayyana cewa gyare-gyaren ba su da nufin sauƙi nan take, sai dai a gina tubalin ci gaba mai ɗorewar.
Shugaban ya buƙaci ƴan ƙasa su rungumi ainihin ma’anar bikin Sallar Layya ta hanyar yin sadaukarwa, da biyayya, da tawali’u kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) ya yi.
Ya buƙaci al’umma da su ɗauki wannan lokaci na Sallah a matsayin dama ta sabunta niyyar aiki tuƙuru don ci gaban ƙasa da zaman lafiya.



