Labarai

Rundunar ƴansandan Abuja ta musanta rahotannin da ke cewa jami’anta sun karɓe iko da hedikwatar jam’iyyar PDP ta Wadata Plaza a ranar Litinin.

Rundunar ta ce tana son “ta nuna cewa babu gaskiya a rahotonnin sannan ba haka al’amarin yake ba, an kai jami’an ƴansandan ne zuwa wurin taron domin wanzar da doka da oda kamar yadda tsarin mulki ya tanada.

A wata sanarwa, rundunar ta ce “babu wani lokaci da jami’an ƴansanda suka kulle sakateriyar jam’iyyar ta PDP.”

A sanarwar, kwamishinan ƴan sanda na Abujar ya buƙaci kafafen yada labarai da su yi kaffa-kaffa wajen tantance labarai kafin su wallafa shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button