Siyasa

INEC ta tantance ƙungiyoyi 14 daga cikin 170 da suka nemi zama jam’iyyun siyasa

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta ware ƙungiyoyi 14 kacal daga cikin ƙungiyoyi fiye da 170 da suka nemi rijistar zama jam’iyyun siyasa a Najeriya.

 

Jami’ar hukumar, Zainab Aminu, ta shaida wa BBC cewa ƙungiyoyin da aka ware sun cika sharuɗɗan farko da aka gindaya, yayin da aka yi watsi da ƙungiyoyi 157 da ba su dace ba.

 

Sai dai ta bayyana cewa hakan ba yana nufin an riga an basu cikakken rijista ba, domin hukumar za ta sake gayyatar su a wani mataki na gaba na tantancewa.

 

> “Za mu sake duba ƙungiyoyin da muka ware domin tabbatar da cewa sun cika dukkan sharuɗɗa – ciki har da samun ofishin ƙungiya, manufofi da sauran abubuwan da doka ta tanada,” in ji ta.

 

 

 

Idan suka wuce wannan mataki na ƙarshe, ne kawai za a amince da su a matsayin jam’iyyun siyasa na

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button