Labarai

Jami’an Hukumar Kula da Hanyoyi ta Jihar Bauchi (BAROTA) Sun Ziyaraci hukumar KAROTA domin koyar sabbin dabarun aiki

Kano, 12 ga Janairu, 2026

 

Wata babbar tawagar jami’an Hukumar Kula da Hanyoyi ta Jihar Bauchi (BAROTA) ta kai ziyara Hukumar Kula da Hanyoyi ta Jihar Kano (KAROTA), da nufin koyon dabarun gudanar da ayyukan hukumar domin inganta zirga-zirgar ababen hawa a jihar Bauchi.

 

Da yake tarbar tawagar a ofishinsa, Manajan Darakta na KAROTA, Hon. Faisal Mahmud Kabir, ya tabbatar musu da cikakken goyon baya da haɗin kai domin cimma manufar ziyarar tasu.

 

 

Hon. Kabir ya bayyana cewa jihar Kano ta shahara wajen zama jagora a kowane fanni na shugabanci, da kuma lamuran da suka shafi inganta rayuwar al’umma ta fuskar tattalin arziki da siyasa.

 

 

Faisal Mahmud ya umurci dukkan sassan KAROTA da su ba tawagar baƙin haɗin kai wajen samar musu da dukkan bayanan da suke buƙata.

 

Shugaban tawagar ta BAROTA, wanda kuma shi ne shugaban hukumar, DCM Zubairu Mato, ya shaida wa Manajan Darakta na KAROTA cewa sun zo Kano ne domin nazarin ayyuka da tsarin aiki na KAROTA, da kuma yadda za su iya aiwatar da irin waɗannan dabarun a jihar Bauchi domin ingantaccen sarrafa zirga-zirgar ababen hawa a kan tituna da manyan hanyoyi.

 

 

DCM Zubairu Mato ya bayyana cewa fannoni kamar samar da kuɗaɗen shiga da kuma aiwatar da dokoki da ƙa’idojin zirga-zirga na daga cikin abubuwan da tawagar za ta fi mayar da hankali a kansu yayin ziyarar tasu

 

 

Ya kuma yaba wa shugabancin KAROTA bisa karimcin da aka nuna musu, tare da fatan za a ci gaba da haɗin gwiwa wajen zirga-zirgar ababen hawa a faɗin jihohinsu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button