Siyasa

Mai bai wa Gwamnan Kano shawara kan tsaro ya sauka daga mukaminsa

Air Commodore (mai ritaya) Salisu Abdullahi Yusha’u Soja ya ajiye mukaminsa na mai bai wa Gwamnan Jihar Kano shawara kan harkokin tsaro (SA Joint Security Services).

 

A cikin wasiƙar murabus ɗin da ya aike wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, mai ɗauke da kwanan watan 26 ga Maris, 2026, Yusha’u ya bayyana cewa murabus ɗin nasa zai fara aiki ne daga ranar 30 ga Maris, 2026.

 

Ya ce matakin da ya ɗauka ya biyo bayan umarnin da ya shafi sabuwar dokar zaɓe ta 2026, wadda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ita, inda aka buƙaci duk masu riƙe da muƙaman gwamnati da ke da burin tsayawa takara su sauka daga mukamansu.

 

Tsohon jami’in sojan saman ya kuma gode wa gwamnan bisa damar da aka ba shi na yi wa al’umma hidima, tare da jaddada ci gaba da biyayya da kuma yi wa gwamnati fatan alheri.

 

Rahotanni na bayyana cewa, dan siyasar na shirin tsayawa takarar majalisar tarayya a mazabar Tudun Wada da Doguwa inda zai kalubalanci Hon. Alhassan Ado Doguwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button