Ketare
Faransa ta kara sa ido a cikin yankinta bayan Isra’ila da Iran sun yi musayar hare-hare masu kisa

Ministan Cikin Gida na Faransa, Bruno Retailleau, ya umarci hukumomin yankin su kara sa ido a fadin kasar, musamman a wuraren ibada, tarukan bukukuwa, da wuraren da ke da alaka da muradun Isra’ila da Amurka, bayan harin da Isra’ila ta kai kan Iran.
Fadace-fadacen sun fara ne bayan wani mummunan hari da Isra’ila ta kai kan wuraren soji da nukiliyar Iran, wanda Tehran ta mayar da martani da harin makamai masu linzami.
Wadannan matakan kariya da aka inganta suna kuma aiki ga “maslaha na Isra’ila da Amurka da kuma wuraren da ke na al’ummar Yahudawa”.
Iran, wanda ta musanta kera makaman nukiliya, ta harba makamai masu linzami masu yawa kan Isra’ila a matsayin ramuwar gayya ga abin da ta bayyana a matsayin “sanarwar yaki.”




