NDLEA Ta Kaddamar da “Operation Sharar Mafaka” a Kano, Ta Kama Mutane 52

Hukumar NDLEA reshen jihar ta ƙaddamar da wani samame na musamman mai suna “Operation Sharar Mafaka” domin tarwatsa wuraren da ake zargin ana safarar miyagun ƙwayoyi a sassa daban-daban na birnin.
Rahotanni daga Martaba FM sun ce an fara aikin ne tun ranar 27 ga Afrilu, inda jami’an hukumar suka kai samame wurare sama da 20 da ake zargi da aikata laifuka.
A ranar farko, an kai farmaki a yankuna kamar Filin Idi, Tashar Rami, Fagge da Farm Centre, inda aka kama mutane 15.
A washegari kuma, an sake kama mutane 16 a wurare kamar Hotoro Flyover da Audu Bako Secretariat.
Haka kuma, an ci gaba da samamen a Kwanar Ungogo da wasu sassan Sabon Gari, inda aka kama karin mutane 21.
Hakan ya sa jimillar wadanda aka kama ta kai 52, ciki har da mata hudu.
Kwamandan NDLEA a Kano, DY Lawal, ya bayyana cewa manufar shirin ita ce rusa wuraren da masu laifi ke fakewa tare da dawo da zaman lafiya, yana mai kira ga al’umma su ba da hadin kai wajen yakar miyagun ƙwayoyi.




