Labarai
Kamfanin mai na ƙasa NNPC, ya bayyana samun ribar Naira biliyan 748 bayan cire haraji a watan Afrilu na shekarar 2025.

Wannan na kunshe cikin rahoton kamfanin na wata-wata, inda kamfanin ya ce ya samu kudaden shiga da suka kai Naira tiriliyan 5.89 a cikin watan.
Kamfanin ya kara da cewa, daga watan Janairu zuwa Maris 2025, ya biya Naira tiriliyan 4.22 a matsayin kudaden da dokar ƙasa ta wajabta masa.
Kazalika rahoton ya ce shirin samar da bututun iskar gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano domin samar da makamashi a arewacin Nijeriya ya kai kashi 75 cikin 100 wajen kammalawa.
Sai dai kuma, sanarwar ta ce dukkan alƙalluma na kuɗi da ta bayar a rahoton na wucin-gadi ne kawai saboda ba a tantance su daga waje ba taukunna.
A fannin samar da mai, NNPC ya bayyana cewa ana fitar da gangar danyen mai miliyan 1.60 a kowace rana a watan Afrilu.



