Hatsari kan hatsari: Yadda matan Gaza ke haihuwa a tagayyare

Duka irin mummunan yaƙin da ke faruwa a Gaza, akan samu haihuwa. To amma sabbin jariran da kuma ƴantayin da har yanzu ke cikin mahaifa na daga cikin waɗanda suka fi shan wahalar yaƙin.
Yayin da ake amun ƙarancin abinci, Majalisar Dinkin Duniya ta ce kowane ɗaya cikin jarirai 10 da aka haifa ba su kai nauuyin da ake buƙata ba, ko ma ba su isa haihuwar ba.
Haka kuma akwai ƙaruwar ɓarin ciki ko haihuwar jariran babu rai da kuma matsalolin lafiyar jarirai.
A asibitin Nasser da ke birnin Khan Younis a kudancin Gaza, Malak Brees, wadda a yanzu ke ɗauke da cikin wata bakwai, tana cikin farbagar harin Isra’ila ko umarnin ficewa daga asibitin ko ma rasa jaririnta.
“Ina fargabar haihuwar jaririn da bai isa haihuwa ba a kowane lokaci daga yanzu, saboda ba ni da wadattaccen sinadarin amniotic da zai taimaka wa jaririna ya girma a cikina,” kamar yadda ta shaida wa BBC.
(https://www.bbc.com/hausa/articles/c2498zrg4mpo?at_campaign=ws_whatsapp)




