Labarai

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce Najeriya ta kasance kasa da har yanzu bata gudanar da cikakken tsarin dimokradiyya, shekaru ashirin da shida da komawa mulkin farar hula.

Fayemi ya yi wannan tsokaci ne a wani shirin gidan Talabijin na Channels da aka gudanar domin tunawa akan ranar dimokuradiyya ta bana.

Ya ce yayin da zabe ya zama wani bangare na kalandar siyasar kasar, har yanzu Najeriya ba ta cika ka’idojin dimokradiyya ba.

Ya amince da ci gaban da aka samu a gwamnatocin baya da na yanzu amma ya nace cewa har yanzu ba a samu zurfin al’adun dimokuradiyya da gyare-gyaren hukumomi ba.

Fayemi ya kuma yi tsokaci kan shekarun da ya yi a matsayinsa na mai fafutukar tabbatar da dimokuradiyya a lokacin mulkin soja, musamman a lokacin mulkin marigayi Janar Sani Abacha.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button