Labarai
Gwamnatin jihar Kano ta karbi rahoton kwamatin binciken kwamishinan kula da harkokin sufuri na Jihar Kano Alhaji Ibrahim Namadi

Idan za’a iya tunawa a makon da ya gabata ne gwamna Yusuf ya kafa wani kwamatin domin binciken kwmashinan kan zargin taka rawa wajen karbar belin mai Safara miyagun Kwayoyi a Kano.
Sakataren gwamnatin Kano Alhaji Umar Farouk Ibrahim ne ya karbi rahoton a madadin gwamnatin Kano.
Sakataren gwamnatin ya ce kamar yadda gwamna Yusuf yake taka tsantsan wajen daukar mutum aiki a kowanne mataki yanzu hanka ma ,idan an samu matsala da mutum sai anbi binciken kwawaf don gani gaskiyar lamarin.




