An samu tsohon shugaban kasar Colombia Alvaro Uribe da laifin karbar cin hanci da rashawa

Tsohon Shugaban Kasar Colombia Alvaro Uribe an same shi da laifin yin katsalandan ga shaidu da cin hanci a wani shari’ar tarihi, inda ya zama tsohon shugaban kasar na farko da aka taba samun laifi a kotu.
Alkalin kotu Sandra Liliana Heredia ta yanke hukunci a ranar Litinin cewa akwai isasshen shaida don tantance cewa Uribe, mai shekaru 73, ya hada kai da wani lauya don yaudarar tsoffin mambobi uku na kungiyoyin ‘yan banga da ke kurkuku su canza shaidar da suka bayar ga Ivan Cepeda, sanata mai ra’ayin riƙau wanda ya kaddamar da bincike kan zargin alakar Uribe da wata kungiyar ‘yan banga a shekarun 1990s.
Shari’ar ta kasance a cikin 2012, lokacin da Uribe ya shigar da kara a kan Cepeda a gaban Kotun Koli. Sai dai a wani yanayi na daban, babbar kotun ta yi watsi da tuhumar da ake yi wa Cepeda tare da fara binciken Uribe a shekarar 2018.
Uribe na fuskantar hukuncin da zai kai har shekaru 12 a kurkuku, amma za a yanke hukuncin a wani zaman kotu daban a ranar Jumma’a. Ana sa ran zai daukaka kara kan hukuncin.




