Adadin mutanen da suka mutu a yakin Isra’ila kan Gaza ya kai kimanin 60,034

Aƙalla Falasdinawa 60,034 ne sojojin Isra’ila suka kashe tun bayan barkewar yaƙin Gaza a watan Oktoba 2023, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta yankin.
An fitar da alkalumman a ranar Talata, inda majiyoyin kiwon lafiya suka shaida wa Al Jazeera cewa akalla Falasdinawa 62, ciki har da masu neman agaji 19, aka kashe tun daga wayewar gari, duk da “dakatarwa” a yakin don isar da muhimman kayan agaji na jin kai.
Rahotanni daga yankin sun nuna cewa Isra’ila ta yi amfani da na’urorin robot da aka yi wa tarko, tare da tankoki da jiragen sama marasa matuki, a cikin abin da mazauna yankin ke bayyana a matsayin daya daga cikin mafi muni na daren da suka gabata a makonnin nan, in ji Tareq Abu Azzoum na Al Jazeera, yana bayar da rahoto daga Deir el-Balah a tsakiyar Gaza.
Sabbin hare-haren sun zo ne yayin da “ake fuskantar matsanancin yanayin yunwa” a Gaza, a cewar wani sabon rahoto daga Tsarin Rarraba Matakan Tsaron Abinci na Duniya (IPC), wani tsarin sa ido kan yunwa na duniya.




