Labarai

Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), reshen Kano ta kama ɗaliban Jami’ar Bayero ta Kano guda 25 da ake zargi da aikata damfara a Intanet.

An kama su ne a ranar Litinin, 21 ga watan Yuli, 2025, a wani samame da jami’an hukumar suka kai kusa da Jami’ar BUK.

Hukumar ta sanar da hakan ne a shafinta na X a ranar Laraba.

Hukumar ta bayyana cewa duk waɗanda aka kama ɗalibai ne a jami’ar, kuma an kama su ne bayan samun sahihan bayanai da ke nuna cewa suna da hannu a aikata damfara ta Intanet.

EFCC ta ce ta bi diddigin waɗanda ake zargin na tsawon makonni kafin kama su, inda aka gano suna aikata damfara ta Intanet, satar bayanan mutane, da kuma dabarar karɓar kuɗi ta hanyar zamba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button