Ketare

Iran ta yi Allah-wadai da ‘dabi’ar wariyar launin fata’ bayan haramcin tafiye-tafiye da Amurka tayiwa wasu kasashen Africa

Iran ta yi tsokaci mai tsanani kan haramcin tafiye-tafiyen da Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya kan ‘yan kasar da na wasu kasashe, tana mai kiran shi “na wariyar launin fata” da kuma alamar kiyayya mai zafi ga ‘yan Iran da Musulmi.

Trump a farkon wannan makon ya rattaba hannu kan wata doka ta zartarwa da ke hana da takaita matafiya daga kasashe 19, ciki har da wasu kasashen Afirka da Gabas ta Tsakiya.

Manufar, wadda za ta fara aiki a ranar Litinin, tana maimaita matakan da aka gabatar a lokacin wa’adin Trump na baya daga 2017-2021. A cikin umarnin zartarwa, Trump ya ce dole ne ya “yi aiki don kare tsaron kasa” na Amurka.

Sabbin takunkumin sun shafi ‘yan ƙasa daga Iran, Afghanistan, Myanmar, Chadi, Jamhuriyar Kwango, Equatorial Guinea, Eritrea, Haiti, Libya, Somaliya, Sudan, da Yemen. An kuma sanya takunkumi mai iyaka ga matafiya daga wasu ƙasashe bakwai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button