Kungiyar ‘yan sandan da suka yi ritaya reshen jihar Kaduna ta ce ta yanke shawarar fara zanga-zanga a fadin kasar nan mai taken “Uwar duk wata zanga-zangar lumana” a ranar 21 ga Yuli, 2025.

Kungiyar ta ce zanga-zangar ta shafi kalubalen fensho ne da ba a warware ba da jami’an ‘yan sandan da suka yi rajista a shirin bayar da gudunmawar fansho ke fuskanta.
Shugaban kungiyar, Mannir M. Zaria da mataimakin shugaban kungiyar, Danlami Maigamo, ne suka bayyana hakan bayan taron da suke yi na wata-wata a wurin taron ‘yan sanda da ke Kaduna.
Jami’an da suka yi ritaya suna neman a fitar da rundunar ‘yan sandan Najeriya daga shirin bayar da gudunmuwar fansho, wanda a cewarsu ya jefa su cikin mawuyacin hali na rashin tattalin arziki, tashin hankali da bakin ciki da mace-mace a tsakanin ma’aikatan da suka yi ritaya.
Kungiyar ta tuno da wata zanga-zangar da reshen kungiyar na jahohin Kaduna da Bauchi ta yi tun daga ranar 24 ga watan Fabrairu zuwa 3 ga Maris, 2025, a zauren Majalisar Dokoki ta kasa, inda aka gabatar da koke ga wasu muhimman ofisoshi guda biyar da suka hada da shugabannin kwamitocin Majalisar Dattawa da na Majalisar da abin ya shafa da kuma Daraktan hukumar DSS.
Sai dai wadanda suka yi ritaya sun nuna rashin jin dadinsu game da shirun da Majalisar ta yi, musamman dangane da sakamakon jin ra’ayin jama’a kan dokar Hukumar Fansho ta ‘yan sanda da aka gudanar a ranar 19 ga Nuwamba, 2024.



