Labarai

Gobara a safiyar yau ta tashi a kasuwar siyar da wayoyi ta Farm center inda ta lalata wani bangare na ginin plazar Dan Sulaika wanda ya janyo asarar miliyoyin naira.

Farm Centre

Rahotanni sun bayana cewar gobarar ta tashi a lokacin da yawancin yan kasuwar basu dawo daga Sallar idi ba.

Da yake zantawa da manema labarai maajin kasuwar Hassan Saminu ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace gobarar tayiwa yawancin masu shaguna a wurin bazata.

Inda ya kara da cewar kafin su ankara tuni ta bazu zuwa wasu shagunan kuma suna zargin haduwar baturin sola da wayar lantarki ne ya janyo tashin gobarar.

Duk da cewar babu asarar rai amma anyi asarar dukiya da dama.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button