Kwankwaso ne ya cancanta ya maye gurbin marigayi Muhammadu Buhari cewar alhaji Aminu Ringim.

Ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar NNPP, Alhaji Aminu Ringim, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, shi ne kaɗai ɗan siyasar da ya cancanta ya maye gurbin marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
A wata hira da manema labarai a Abuja, Ringim ya ce irin ayyukan ci gaban ɗan Adam da na gine-gine da Kwankwaso ya yi a lokacin gwamnatinsa a Kano ne suka tabbatar da cancantarsa.
Ya kwatanta Kwankwaso da fitattun shugabannin arewa kamar Sir Ahmadu Bello da Malam Aminu Kano, yana mai cewa ya tsaya tsayin daka wajen kare ‘yan ƙasa marasa ƙarfi.
Ringim ya bayyana Kwankwaso a matsayin ɗan siyasa na ƙasa baki ɗaya wanda ke da goyon baya a jihohin da suka haɗa da Katsina, Jigawa, Zamfara, Sokoto, da Kebbi, yana mai cewa irin tasirin da ya ke da shi ya zarce na jihohi ko yankuna.
Ya jaddada cewa Kwankwaso ba wai kawai yana magana kan sauyi ba ne, ya kuma aiwatar da shi lokacin da ya kasance gwamna da kuma Ministan Tsaro.
Daga cikin manyan ayyukansa akwai ilimi kyauta, da tallafin karatu na waje, da horon sana’o’in dogaro da kai.



